Saturday, February 27, 2010

Duniya mai tafiya da zamani

Lalle kam yanzu duniya a tafin hannun mu take kamar yadda masana ke fadi, a tunani na yanzu babu dan kauye saboda fitowar wayar salola tana dada wayarwa da jama'a kai wasu ma makaranta suke komawa domin kada ai musu sakiyar daba ruwa. Karin dadawa birni da kauye na amfani da wayar salola ne domin sada zumunci ta hanya mai sauki, musamman yadda aka sami zauruka na tattauna wata mahawar irin su facebook, twitter, kai harda gagaruma gudummawar gidajen rediyoyin kasashen waje masu yadda harshen hausa, kamar su Bbc hausa dake london, Voa hausa dake America. A nan sai muyi musu babbar godiya a garesu. Bissalam. Aliyu M Umar Kwalli Kn.